A yayin da ya ke sanar da matakin a Enugu, Onwuka ya zana sunan Farfesa Chukwuma Solodu a matsayin Gwamnan Babban Banki da Farfesa Pat Utomi a matsayin ministan harkokin waje, da Farfesa Jerry Gana a matsayin ministan sufuri sai Labaran Maku a matsayin ministan sufurin sama da kuma Oruma Oteh a matsayin Ministan kudi.
Akwai Benny Lar da aka nada sakataren gwamnati tare da nada wasu a matsayin jekadun Biafra a Amurka da wasu manyan kasashen duniya.
Mista Onwuka ya ce gwamnatin rikon kwaryar za ta yi aiki ne nan da wata daya daga ranar 1 ga Agusta.
Sannan a cikin sanarwar ya ce Isra’ila ce za ta samar da tsaro a Biafra yayin da kuma kamfanonin Amurka za su tafiyar da harakar arzikin mai a yankin.
Fafutikar kafa kasar Biafra ya taba jefa Najeriya cikin yakin basasa a 1967 zuwa 1970 al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan Miliyan daya.
Wasu Kungiyoyin matasan arewacin Najeriya sun bukaci Gwamnatin kasar ta gaggauta daukar mataki kan ‘Yan Biafra da suka sanar da kafa Gwamnati.288